-
Hadiza Abdullahi posted an update
MATUKAR AKWAI MUTUM BIYAR A KARKASHIN KA, DOLE SAI KA KASHE SAMA DA N180,000 DUK WATA KODA KUWA BASHI ZA KA CI.
Assalamu Alaikum!
A dogon nazari da nayi ga me da mafi sauqin rayuwar da talaka zai yi matukar yana da Mutum biyar karkashinsa, na gano cewa dole duk wata ya kashe sama da N180,000 Koda kuwa bashi zai ci domin cike gibin abunda yake samu.
A wannan rubutun nayi la’akari da girki biyu Kacal. Wato girkin rana da Kuma girkin dare.
1. Girkin Rana
Matukar Kun kai Mutum biyar a gidanku mafi Karanci ku ci
a) Taliya Daya da Rabi N1575
b) Maggi N200
c) Mai Oil N300
d) Kayan Miya N200
e) Gawayi N100
Total: N2,275
Kudin Kwana talatin: N2,275 x 30 = N68,250
2. Girkin Dare
(I) Bangaren Tuwo
A bangaren girkin dare, nayi lissafin yadda za mu yi amfani da ragowar tuwon dare domin yin dumame.
a) Gari rabin Kwano N1750
b) Mai Oil N300
c) Maggi N200
d) Kuka N200
e) Daddawa N100
f) Kayan Miya N100
g) Gawayi N200
Total: N2,850
Kudin Kwana talatin: N2,850 x 30 = N85,500
(II) Bangaren Koko tunda tuwon bazai isa da safe ba
Koko babu sugar N500
Kudin Kwana talatin: N500 x 30 = N15,000
(III) Omo da Sabulu
Omo Kullum N100
Kudin Kwana talatin N100 x 30 = N3000
Sabulu Eva: 550 sau biyu = N1,100
(IV) Kudin Wuta
N4000
(V) Kudin Ruwa
Jarka Shida 50 x 6 = N300
Kudin Kwana talatin: N300 x 30 = N9,000
OVERALL TOTAL: N185,850
JAN HANKALI
1. Babu kudin zuwa Aiki a matsayin ma’aikaci
2. Babu Maganar lafiya
3. Babu Maganar kudin Haya
4. Babu Maganar kudin makarantar yara
5. Babu Maganar Kifi, Nama, Apple da sauran kayan marmari
6. Babu kudin Kayan sakawa
Wannan lissafin shine qarshen rayuwar da man Talaka zai iya a Najeriya amman Ko Ma’aikaci Mai Level 14 baya daukar wannan albashin matakin Jiha ballantana Kananun ma’aikata. Rayuwa tayi matukar tsada. Mutane na mutuwa saboda yunwa, da Tsananin Rashin Lafiya, ga shi Kuma babu wani alamar sauqi daga wajen shugabannin mu.
Allah ka kawo mana mafita, Allah ka kawo mana shugabannni masu tausayi da Jin kan man Talaka. Allah mun Tuba. Ka Dube Mu.
Joseph and Haruna-
Amen
-