• Duk yadda Dan adam ya ke, kar ka sake ka wulakantashi.

      Duk yadda ka kai ga daukaka, kar ka ce za ka tabbata a cikin daula

      Duk yadda ka kai ga talauci, kar ka yi tunanin haka za ka mutu

      Babu wani abun da ya ke tabbata dindindin. Amma Allah kawai, maras farko, maras karshe.

      Rayuwarmu da lamuranmu duk a hanun Allah mahaliccinmu ya ke. Shi kuma ya na amfani da kalmarnan ta kumfa yakun.

      Allah mu na rokonka sitira da duk wani alheran Duniya, ka nufe mu da tuba kafin mutuwa. Allah Ka mana arziki da gidan Aljannah

      Like
      Hussain Miga
      2 Comments